“Gudummawar Dokoki ta Sanata Ibrahim Khalid a Majalisar Tarayya ta 10.”
Sanata Ibrahim Khalid, wakilin da ake Alfahari da shi a Shiyar Kaduna Zone 1, ya nuna cikakken jajircewar sa wajen kula da jin daɗin jama’a da ci gaban al’ummarsa, ta hanyar ƙoƙarin ƙirƙirar dokoki masu amfani. A tsawon zaman sa a Majalisar Tarayya ta 10, Sanata Khalid ya jagoran ci gabatar da muhimman kudurori da nufin samar da ci gaba mai ɗore wa, da kuma magance matsalolin da ke addabar mazabar sa da kuma ƙasar baki ɗaya.
“Ga taƙaitaccen bayani kan muhimman kudurorin da Sanata Khalid ya dauki nauyinsu.”
“Kowacce Doka an tsara ne domin kawo sauyi mai ɗorewa, da kuma ci gaban Jihar Kaduna da kuma ga daukacin al’ummar Najeriya.”
SB.214: Dokar Kafa Kwalejin Kimiyyar Amfanin Gona da Fasahar Abinci ta Tarayya, Lere, Jihar Kaduna (2023)
A ranar Alhamis, 2 ga watan Nuwamba, 2023, Sanata Khalid ya gabatar da kudurin dokar kafa Kwalejin Kimiyyar Amfanin Gona da Fasahar Abinci ta Tarayya a Lere, Jihar Kaduna. Wannan shiri yana da nufin bunkasa ilimi da bincike binciken bunkasa fannin noma, tare da bai wa matasa damar zama masana da masu kirkire-kirkire a harkar noma. Kwalejin da ake shirin kafawa za ta mayar da hankali kan kimiyyar amfanin gona, domin karfafa bunkasa ingantaccen abinci da habaka samar da amfanin gona mai dinbin yawa — muhimman ginshikai ne wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar mu Kaduna. Da Najeriya baki daya.
SB.307: Kudurin Dokar Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (2024)
A ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, 2024, Sanata Khalid ya gabatar da muhimmin kudurin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999. Wannan kuduri yana da nufin yin sauye-sauyen da suka dace domin karfafa tsarin dimokuradiyya, inganta mulki, da tabbatar da gaskiya da rikon amana. Ana sa ran waɗannan sauye-sauyen za su haifar da gwamnati mai saurin amsa bukatun jama’a, wacce ke cika muradun ‘yan Najeriya.
SB.305: Kudurin Dokar Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (2024)
A ci gaba da jajircewar sa wajen gyaran kundin tsarin mulki, a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024, ya gabatar da kudurin SB.305 wanda ke neman ƙarin sauye-sauye a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya. Kudurin yana da nufin magance sabbin matsalolin shugabanci, inganta rabon iko daga matakin tarayya zuwa matakan ƙasa, da kuma karfafa ci gaba mai adalci a dukkan yankuna. Waɗannan gyare-gyare za su bai wa kananan hukumomi da al’umma ƙarfi, domin samar da ci gaban da zai shafi kowa da kowa a fadin ƙasar nan.
SB.529: Kudurin Dokar Kafa Jami'ar Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Shehu Idris, Makarfi (2024)
A ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024, Sanata Khalid ya gabatar da Kudurin Dokar Kafa Jami’ar Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Shehu Idris. Wannan kuduri yana neman kafa wata cibiya ta zamani a Makarfi, Karamar Hukumar Makarfi, Jihar Kaduna, da za ta mayar da hankali kan bunkasa ilimi da bincike a fannin kimiyyar lafiya. Ta hanyar bunkasa da fifita fasahar lafiya, jami’ar na da nufin samar da ƙwararrun ma’aikatan jinya da masu kirkire-kirkire domin fuskantar ƙalubalen da ke addabar fannin lafiya a Kasar mu Najeriya.
SB.243: Kudurin Dokar Kafa Asusun Tallafawa Asibitocin Manyan Makarantu (2023)
A ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, Sanata Khalid ya gabatar da Kudurin Dokar Asusun Tallafawa Asibitocin Manyan Makarantu. Wannan kuduri yana da nufin kafa wani asusu na musamman domin tallafa wa asibitocin manyan makarantu a duka fadin ƙasan nan, domin tabbatar da cewa an samar musu da kayan aiki da ababen da suka dace don bayar da ingantaccen kulawar lafiya ta zamani. Ta hanyar inganta gine-gine da kayan aiki a irin wadannan asibitoci, Sanata Khalid na fatan kara habaka samun kulawar lafiya mai inganci ga daukacin jama’an Najeriya.
SB.170: Kudurin Dokar Kafa Kwalejin Koyon Harkokin Fasaha ta Tarayya, Saminaka, Jihar Kaduna (2024)
Sanata Khalid ya ci gaba da fafutukar kawo ci gaba ta fannin ilimi a mazabarsa ta hanyar gabatar da Kudurin Dokar Kafa Kwalejin Koyon Harkokin Fasaha ta Tarayya, Saminaka, a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, 2024. Kudurin na da nufin kafa wata cibiyar ilimi ta tarayya da za ta mayar da hankali kan ilimin fasaha. Wannan mataki yana da burin magance karancin ma’aikatan da ke da ƙwarewa, da kuma karfafa ilimin fasaha, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ƙwararrun ma’aikata masu tasiri a fannin fashaha da kirkire a Jihar Kaduna da kuma ƙasa baki ɗaya.
SB.475: Kudurin Dokar Kafa Asusun Tallafawa Waɗanda Suka Shiga Cikin Halin Ƙuncin Ta’addanci da Garkuwa da Mutane (2024)
A ranar Talata, 11 ga watan Yuni, 2024, Sanata Khalid ya gabatar da Kudurin Dokar Kafa Asusun Tallafa wa Waɗanda Suka Shiga Cikin Halin Ƙuncin Ta’addanci da Garkuwa da Mutane. Wannan kuduri yana da nufin kafa wani asusu na musamman domin tallafawa waɗanda suka tsinci kansu a cikin wannan yanayi, ta hanyar ba su tallafi na kuɗi, magani, da samar da kwararrun masu ilimin rayuwa domin taimaka musu wajen sake gina rayuwar su. Wannan shiri yana mayar da martani kai tsaye ga ƙalubalen rashin tsaro da ake fuskanta, kuma yana da nufin kawo sauƙi da adalci ga iyalan da abin ya shafa.
SB.528: Kudurin Gyaran Dokar Cibiyoyin Lafiya na Tarayya (2024)
A ci gaba da ƙoƙarin sa na gyara fannin lafiya, a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, 2024, Sanata Khalid ya dauki nauyin gabatar da Kudurin Gyaran Dokar Cibiyoyin Lafiya na Tarayya. Wannan kuduri yana da nufin gyara dokar da ta kafa Cibiyoyin Lafiya na Tarayya domin samar da ingantattun tsarin shugabanci da gudanar wa a fadin Najeriya. Gyaran dokar zai taimaka wajen inganta ingancin kulawar lafiya, tabbatar da nagartattun hanyoyin gudanarwa, da kuma faɗaɗa samun damar kula da lafiya ga jama’a a fadin ƙasar nan.
“Jajicewa a bisa manufar ku, Jagoranci tare da kyawawan Manufa.”
Sanata Ibrahim Khalid
Ayyukansa na majalisa shaida ne ga jajircewar sa wajen inganta rayuwar al’ummar sa da ‘yan Najeriya baki ɗaya. Tun daka fannin ilimi da lafiya zuwa tsaro da shugabanci, kudurorin sa an tsara su ne domin magance manyan ƙalubalen da ake fuskanta a yau, da kuma shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗore wa a nan gaba. Sanata Khalid na ci gaba da aiki tukuru domin cigaban Jihar Kaduna da ƙasar Mu Najeriya baki ɗaya, yana tabbatar da cewa kowanne kudurin doka yana da ma’ana a tafiyar da ci gaban ƙasar mu.